Sunday, 19 August 2018

An kirkiro manhajar da za ta rage batan alhazai lokacin Hajji

Hukumar kula da aikin Hajjin Najeriya ta ce ta kirkiri wata manhaja da za ta taimaka wajen rage batan alhazai yayin zaman Mina. Hukumar ta ce manhajar ta GPS za ta dinga nuna wa alhazai taswirar wajen da suke da kuma inda suke nema.Manhajar tana dauke da shafin intanet kuma an saya ta a dukkan shemomin jihohin kasar, ta yadda za a iya latsa duk wacce mutum ke nema daga ko ina, kamar filin Arfa da Muzdalifa da wajen jifa.


Kuma nan take za ta nuna wa mutum taswirar inda zai bi ta manhajar Goggle map.

Sai dai manhajar za ta dinga aiki ne kawai a wayoyin komai da ruwanka. Hukumar ta NAHCON ta ce ta kuma samar da wasu lambobin waya da alhazai za su iya kira ba dare ba rana domin neman taimako. Shugaban hukumar at NAHCON Abdullahi Mulhtar ya yi kira ga duk alhajin da ya kira lambar ba a saurare shi ba, ya kai korafi.

A kowace shekara daruruwan alhazai ne ke bata, inda suke shan bakar wahala tsakanin shemomi yayin neman tantinansu.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment