Sunday, 12 August 2018

An kwantar da Ronaldo a Asibiti

Tsohon tauraron kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da kuma Brazil, Ronaldo Nazario ya kwanta a asibiti bayan yayi fama da mura me tsanani.


Rahotanni sun bayyana cewa an kwantar da Ronaldon a wani asibitin gwamnati inda yake samun kulawar gaggawa amma daga baya aka mayar dashi wani asibitin kudi.

Ronaldon ya tabbatar da wannan labari inda ya bayyana a dandalinshi na Twitter cewa, yayi fama da mura wadda tasa aka kwantar dashi a asibiti tun ranar Juma'a amma gobe, Litinin za'a sallameshi ya koma gida.

Ya karkare da cewa, yana godiya da irin soyayyar da aka nuna mishi.

No comments:

Post a Comment