Sunday, 26 August 2018

Ana bikin #RanarHausa a shafukan zumunta

Ma'abota shafukan sada zumunta na zamani na bikin ranar Hausa ranar Lahadi.

Wani mai fafutika a shafukan zumunta kuma mai sha'awar inganta harshen Hausa, Abdulbaqi Jari da wasu abokansa ne suka kirkiro ta domin raya harshen Hausa da kuma inganta amfani da shi a kan shafukan sada zumunta. Ana gudanar da bikin #RanarHausa a kowacce ranar 26 ga watan Agusta.


An fara bikin ne a shekarar 2015, inda a wannan shekara ta 2018, ake yin sa karo na hudu.

Bayan shafukan sada zumunta, ana gudanar da hira a dandali daban-daban da kuma gidajen watsa labarai. A kowacce shekara kimanin makwanni biyu zuwa ranar, ana ba wa ranar take domin ba da muhimmanci wajen tattaunawar.

Taken wannan shekarar shi ne "Shigar da kirkire-kirkiren zamani cikin rayuwar Hausawa".
Abdulbaqi Jari ya yi kira ga kamfanin Twitter da Instagram su shigar da harshen Hausa cikin harsunan amfani a kan shafukansu saboda girman harshen da kuma yawan masu amfani da shi a nahiyar Afirka.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment