Thursday, 9 August 2018

Ana makarkashiyar tsige Buhari a Majalisa>>Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa a Najeriya, Bola Tinubu ya yi zargin cewa, wasu mambobin Majalisar Dokokin Kasar na kitsa makarkashiyar tsige shugaba Muhammadu Buhari daga kujerarsa.


Tinubu ya gargadi masu kitsa makarkashiyar da su yi watsi da mummunar aniyarsu saboda ba abu ba ne mai yiwuwa "kadangare ya yi kokuwa da barewa."

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Laraba a yayin taron bikin sauya shekarar tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan Kasar, Godswill Akpabio daga PDP zuwa APC a jihar Akwa Ibom da ke kudancin kasar.

Jagoran ya bayyana abin da ke faruwa yanzu haka a kasar a matsayin yaki tsakanin bangarorin da ke fafutukar samun ci gaba da kuma masu tsattsauran ra’ayi.

"Mun yi amanna da gwamnatin al’umma, wadda al’umma ta zaba, amma masu tsattsauran ra’ayi sun yi amanna da gwamnatin rarraba dukiyar al’umma da wawure ta. In ji Tinubu.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment