Friday, 17 August 2018

Anyi zanga-zangar nuna goyon bayan shugaba Buhari a Landan

Wasu 'yan Najeriya a birnin Landan sunyi gangamin nuna goyon baya ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da mataimakinshi, Farfesa, Yemi Osinbajo, mutanen sunyi gangaminne a gaban gidan da shugaban ke hutu da ake kira da gidan Abuja.


Sun bayyana cewa suna goyon bayan shugaba Buhari a bisa kyawawan ayyukan da yake a kasarnan kuma suna fatan zai ci gaba da haka.

Sun kuma ce suna goyon bayanshi da Osinbajo a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu.
Wannan gangamin na zuwane kwanaki kadan bayan da wasu su kuma dake adawa da salon mulkin na  Buhari sukayi tasu zanga-zangar a can birnin Landan din.

Inda suka yi kira da cewa, ya koma Najeriya ya rika jiyyar rashin lafiyarshi a irin asibitocin da ya ginawa 'yan Najeriyar.

Sun kara da cewa, ai kasashen da sukaci gaba ne ke da Asibitoci masu kyau, dan haka ya koma gida ya ciyar da Najeriya gaba.


No comments:

Post a Comment