Thursday, 16 August 2018

Arewacin Najeriyane mafi ci baya a Duniya>>Nuhu Ribado

Tsohon shugaban hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC,  Malam Nuhu Ribado ya bayyana cewa, Arewacin, Najeriyane mafi ci baya a Duniya.


Ribadu ya bayyana hakane a gurin taron kaddamar da wani littafi da akayi, jiya, Laraba a babban birnin tarayya, Abuja.

Ya bayyana Almajiranci da mafi munin cin zarafin dan Adam.

The Cable ta ruwaito cewa, Ribadu yace ya fitone daga Yola kuma irin al-adunmu daya da jihohin Kano da Kaduna amma bamu da Almajirai kuma muma musulmine. Almajiranci cin zarafin dan adam ne amma duk da haka wasu na kareshi da fadin cewa suma irin karatun da sukayi kenan.

Ya bayar da misali inda yace yayi aiki da kwamiti daban-daban akan binciken rikice-rikicen da suka faru a Arewacin Najeriya, misali fadan Shri'a da akayi a Kaduna a shekarar 2000.

Yace akwai inda suka je aka bude musu wasu kabari inda aka binne kananan yara wanda babu wanda yasan sunan ko guda daya daga cikinsu, yace, irin abinda ya gani a wannan kabari har yanzu ya kasa mantawa dashi.

Ya koma gurin wadanda suka binne gawarwakin yaran ya tambayesu ko sun san sunan yaran? Sukace a'!a, ya kara tambaya ko sunsan wanene malaminsu, sukace a'a, ya kara tambaya akwai wanda ya kawo musu cigiyar batan danshi? sukace a'a.

Yace wannan abu ya bata mishi rai.

Sannan wata rana zashi kasar waje, ya shiga jirgin sama, sai ga 'ya'yan gwamnan da ya kawo shari'a Najeriya a cikin jirgi, yace, yana ganinsu sai tunanin wadancan yara da aka binne ya fado mishi, babu wanda yayi magana akansu, malaminsu ko iyayensu babu wanda ya nemi inda suke.

Yace ya kamata a duba lamarin Almajiranci idan ba haka ba ba zamu taba shawo kan matsalolin da muke fama da suba.

No comments:

Post a Comment