Friday, 24 August 2018

Ashe Abu Bakr Al-Baghdadi na nan da ransa?

Wani sabon sako na sauti da kungiyar IS ta fitar na cewa shugaban kungiyar Abu Bakr Al-Baghdadi na nan da ransa, kuma kungiyar na shirin kai wasu hare-hare akan kasashen yammacin Turai.


Idan aka tabbatar da sahihancin wannan sakon, to zai kasance karo na farko kenan da aka ji duriyarsa a kusan shekara guda.

Kungiyar ta IS ta taba mamaye yankuna masu yawa a kasashen Siriya da Iraki, kuma ta rika kai hare-hare a cikin wasu kasashen Turai.

Hukumomin tsaro na kasa-da-kasa sun ayyana al Baghdadi a matsayin mutumin da aka fi nema ruwa a jallo.

A cikin sakon na sauti, ya yi kokarin nisanta kansa daga gagarumar asarar da kungiyarsa ta tafka a shekarar da ta gabata.

Ya ce koma baya ne kawai da ba shi da nasaba da rashin yankunan da aka kwace daga kungiyar.

Ya kuma yi kokarin karfafa gwuiwoyin mayakan kungiyar ta IS.

An dai sami wasu rahotanni da ke cewa an hallaka shugaban na IS ne a wani harin da Rasha ta kai da jiragen yaki., amma kafofin leken asiri na Amurka da Iraqi na da ganin yana nan da ransa.

Wani kawancen kasashe a karkashin jagorancin kasashen Turai shekara hudu da ta gabata ya yi wa kungiyar mummunar illa, inda har ta rasa yankunan da ta ke rike da su baki daya.
Amma wani sabon kiyasi na nuna cewa kungiyar na da mayaka da suka fi mutum 20,000 a cikin Siriya da Iraki.
BBCHausa.

No comments:

Post a Comment