Friday, 17 August 2018

Ashe Oshiomhole ya taba dukawa Saraki

Tun bayan da kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ya canja sheka daga jam'iyya me mulki ta APC zuwa babbar jam'iyyar adawa ta PDP ake cece-kuce akan saifa ya hakura da kujerarshi.


Maganar ta fara zafi ta yanda har Sarakin da shugaban APC, Adams Oshiomhole suke musayar kalamai.

Wannan hoton na sama da aka dauka a shekarun baya daya nuna Oshiomhole na dukawa Saraki, ya dauki hankulan mutane a shafukan sada zumunta inda da dama sukace siyasa kenan.

No comments:

Post a Comment