Friday, 31 August 2018

Atiku Abubakar ya zubar da hawaye kan kalubalen da kasar ke fuskanta


Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya koka kan kalubalen da kasar ke fuskanta yayinda kungiyoyi da dama suka siya tare da gabatar masa da fam din tsayawa takara shugabancin kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, jaridar Daily Trust ta ruwaito.


Lamarin ya sosa ran tsohon mataimakin shugaban kasarlokacin da wata mai suna Princess Adekem Adesanya ta gabatar da jawabinta akan kalublen da kasar ke fuskanta a yanzu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, Atiku ya fashe da kuka inda yace gwamnatinsa zata gyara Najeriya zuwa tafarkin cigaba idan har aka zabe shi.
Naija.ng

No comments:

Post a Comment