Friday, 17 August 2018

Ba a biya kudi ba kafin sako 'yan matan Dapchi>>Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ta biya mayakan Boko Haram 'makudan kudin fansa' kafin su sako 'yan matan Dapchi.


Wani rahoto ne da aka gabatar a gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa sai da gwamnatin kasar ta biya "makudan kudi" don kubutar da 'yan matan makarantar sakandaren garin Dapchi.

Har ila yau rahoton ya ce irin wadannnan kudaden da ake biya suna kara taimakawa wajen wanzuwar ayyukan ta'addanci a yankin Tafkin Chadi.

Fiye da 'yan mata 100 ne wani bangare na kungiyar Boko Haram ya sace a wata makarantar sakandaren garin Dapchi a jihar Yobe a watan Fabrairun da ya gabata.

Sai dai kimanin 'yan mata 105 kungiyar ta saki daga bisani, amma kawo yanzu akwai guda da ta rage a hannun mayakan kungiyar wato Leah Sharibu.

Bayan soko 'yan matan dai Ministan Yada Labaran kasar Lai Mohammed ya shaida wa manema labarai cewa, ba a biya ko da sisin kwabo ba, gabanin sako 'yan matan a watan Maris din da ya gabata.

Hakazalika bayan fitar rahotan Majalisar Dinkin Duniyar, a ranar Alhamis ministan ya kara jaddada matsayinsa na farko.

"Bai kamata wani ya ce Najeriya ta biya kudi kafin ceto 'yan matan Dapchi, ba tare da nuna kwararan hujjoji da za su tabbatar da hakan ba," kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka masa Segun Adeyemi ya fitar ta ce.

Lai ya kalubanci duk wani da ke hujjoji da ke nuna cewa an biya kudin da ya bayyana wa duniya hakan.

Har ila yau ya ce "to idan kuma babu hujjojin da za su gasgata hakan to abin ya zama shashi-fadi ke nan."
BBChausa

No comments:

Post a Comment