Sunday, 26 August 2018

Ba Wajen Buhari Ba Ko Ina Zaka Je Ka Ci Taliyar Karshe>>El-Rufa'i Ga Shehu Sani

Ba Wajen Buhari Ba Ko Ina Zaka Je Ka Ci Taliyar Karshe - El-Rufa'i Ga Shehu Sani 
Kwana ɗaya bayan ziyarar da Sanata Shehu Sani ya kai wa shugaban 'kasa a mahaifarsa, Gwamna El-Rufa'i ya bayyana wa masu ruwa da tsakin jam'iyar cewa ba zai taɓa sauraren sanatan ba har sai ya samo wa Jihar Kaduna bashin Dala miliyan 350. 


Gwamnan ya bayyana wa masu ruwa da tsakin jam'iyar hakan yayin da yake masu jawabi a 'karamar hukumar Kaduna North. 

Gwamnan ya ce: "Ba zai taɓa yiwuwa ba ka ɓoye zaɓinka a cikin siyasa. Jami'an gwamnati suna da zaɓinsu amma ita gwamnati ba ta da ɗan takara. Dukkan wanda kuka zaɓa, zaɓin Allah ne.

"Amma kamar yadda dukkanku kuka sani, ina da ɗan takarana a nan. Za ku iya tunawa da cewar mun zaɓi wani wai shi Shehu Sani a zaɓen da ya gabata. Bayan ya je ya sha ruwan Abuja, sai ya fara abubuwan da basu dace ba. Shi ne cin zarafin shugaban 'kasa da jam'iyarsa tare da yi wa jam'iyar zagon 'kasa.

"Hakan ne ya sa ni da kaina na ce da Uba Sani ya yi takara da shi. Don haka Uba Sani ne ɗan takarana.

"Kamar yadda duk kuka sani, Shehu Sani na daga cikin sanatocin da suka yi wa Jihar Kaduna bu'kulun samun bashi. Tun da ya nuna wa mutanen Kaduna wannan 'kiyayyar, dole ku saka masa da abin da ya aikata maku a zaɓen fitar da gwani na jam'iya.

"Saboda haka ina neman alfarma a gurinku da ku goya wa Uba Sani baya a zaɓen fitar da gwani.

"Mun yi mamaki da Shehu Sani bai bar jam'iyar ba. Mun yi zaton shima zai yi riddar siyasa kamar yadda wasu suka yi. Amma ya zauna a jam'iyar yana 'ko'karin gyara kurakuransa.

"Muna saurarensa. Kamar yadda na ce, ba mu da 'korafi a kansa, sai dai a kan ɗabi'unsa. Idan ya gyara, za mu saurare shi. Amma idan ya 'ki samo wa Jihar Kaduna bashin nan na Dala miliyan 350, to ba za mu saurare shi ba.

"Ya kamata makusantansa su gaya masa cewa, duk inda zai je (neman kamun 'kafa), ba za mu saurare shi ba mutu'kar bai kawo Dala miliyan 350 Kaduna ba."

MAJIYA: Daily Nigerian

No comments:

Post a Comment