Wednesday, 8 August 2018

'Ba zamu ga gurbin Cristiano Ronaldo ba'

Bayan wasan da suka buga, Real Madrid da AS Roma wanda aka tashi Madrid din tayi nasara da ci 2-1, dan wasan ta na tsakiya, Dani Ceballos yace, kwata-kwata ba zasu ga gurbin Cristiano Ronaldo ba.


Da yake hira da manema labarai bayan kammala wasan, Ceballos ya bayyana cewa, Marcos Asensio, Gareth Bale da Karim Benzema nada kwarewar da zasu shafe rashin Cristiano Ronaldo a kungiyar.

Ya kara da cewa, idan kuka lura yanzu yanayin wasanmu ya canja ba irin na da bane, wadannan 'yan wasan uku suna kai hari sosai kuma muna rike kwallo yanda ya kamata, ba zama ka taba sanin cewa babu Ronaldo a kungiyar ba, kamar yanda Marca ta ruwaito.

No comments:

Post a Comment