Thursday, 2 August 2018

Ba Zan Sauka Daga Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa Ba>>Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya yi ikirarin cewa ba zai sauka daga kujerar shugabancin majalisar Dattawa ba duk da yake ya canja sheka zuwa jam'iyyar PDP.


Shugaban jam'iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole ne dai ya nemi Saraki ya sauka daga kujerar shugabancin majalisar wadda a bisa ka'ida, dan majalisar APC ne ya cancanci kujerar saboda har yanzu, APC ce ke da rinjaye a majalisar inda take da sanatoci 53.

No comments:

Post a Comment