Sunday, 12 August 2018

'Babu dan shugaban kasa dake aiki a NNPC'>>Bashir Ahmed

Wani mutum a dandalin shafin Twitter me suna Broda Ayo, yayi zargin cewa daya daga cikin 'ya'yan shugaban kasa na daga cikin masu gudanarwa na kamfanin mai na kasa, NNPC, inda har yace, Albashinta ya kai sama da miliyan shida.


To saidai me baiwa shugaban kasa shawara ta fannin sabbin kafafen sadarwa, Bashir Ahmed ya karyata wancan ikirari inda yace, Ka daina gayawa mutane labarin karya Ayo, abinda ya fada ba haka yake ba babu koda guda daga 'ya'yan shugaban kasa dake cikin masu gudanarwa na kamfanin NNPC.

No comments:

Post a Comment