Thursday, 2 August 2018

Babu wanda zai kara fita daga APC>>Gwamnonin APC

Shugaban Kungiyar Gwamnonin jam'iyyar APC a Najeriya Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya ce babu wani da zai kara fita daga jam'iyyar.


Gwamnan ya ba da wannan tabbacin ne lokacin da yake magana da manema labarai bayan wata ganawa da gwamnonin jam'iyyar suka yi da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da wadansu gwamnoni uku ne a baya-bayan nan suka sauya sheka daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Amma gwamnonin APC 22 sun bai wa Shugaba Buhari da kuma Shugaban jam'iyyar Adams Oshiomhole tabbacin samun nasara a zaben shekarar 2019 a jihohinsu.

"Har yanzu muna da karfi kuma kawunanmu a hade suke. Muna da iko a jihohi 22 da sanatoci 53. Har yanzu mu ne ke da rinjaye. Kuma muna fatan samun karin jama'a a jam'iyyarmu," in ji Gwamna Rochas.

Ya ci gaba da cewa "Mun bai wa shugaban kasa tabbacin cewa muna tare da shi. Kuma babu wani mutum da zai kara fita jam'iyyar. Muna ba 'yan Najeriya tabbacin cewa mu ne za mu sake yin nasara a zaben shekarar 2019."

An yi ganawar ce gabanin hutun kwana 10 da shugaban zai fara a ranar Juma'a a birnin Landan.

Shugaban ya yi ganawar ne sa'o'i kadan bayan Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal ya sanar da koma wa jam'iyyar PDP daga APC, wato ya bi sahun takwarorinsa na jihohin Kwara da Benue.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment