Wednesday, 8 August 2018

Barcelona sun ba Man U 'yan wasa biyu da miliyan 45 ta basu Pogba amma tace bata yadda ba

Maganar siyen tauraron dan kwallon kafar Manchester United, Paul Pogba da Barcelona ke son yi na kara yin karfi kuma ta nuna da gaske take, domin kuwa zuwa yanzu Barca ta bayar da 'yan wasanta guda biyu da kudi Yuro miliyan 45 akan Pogban amma Man U tace bata yadda ba.


A bara, lokacin da aka bude kasuwar saye da sayarwar 'yan wasa, Manchester United ta nuna son sayen Andre Gomes, a bana kuma ta nuna tana son sayen Yerry Mina wanda duka 'yan kwallon Barca ne, shine Barca tayi amfani da wannan dama ta baiwa Man U din 'yan wasan guda biyu da kudi Yuro miliyan 45 dan a bata Pogba amma Man U tace, inaaa, bata yadda da wannan zancenba, ko kusa ba zata sayar da Pogba a haka ba.

Masoyan kungiyar Man U suma ba'a barsu a baya ba wajan magana akan wannan ciniki inda da dama suka shiga shafukansu na yanar gizo suna wa Barca tsiya da cewa lallai kudi ya kare mata.

Wani yace to ai koda ace kudin da Barca ta bayar ya kai Yuro miliyan 50 to ko me askin Pogban ba za'a sayar musu akan hakan ba.

Wani kuwa cewa yayi lallai kudi sun karewa Barcelona.

Pogba dai ya taimakawa kasarshi ta Faransa cin kofin Duniyar 2018 wannan yasa ya kara haskakawa akan wadda yake yi a Duniya.

Saidai wani rahoton The Mail na cewa, Pogban ya riga ya amincewa Barcelona cewa zai buga mata wasa harma ya gayawa abokan aikinshi dama masu gudanarwa na kungiyar Man U din.

No comments:

Post a Comment