Thursday, 16 August 2018

Bayan da Madrid tasha kashi a hannun Atletico Madrid, Wani dan wasanta yace>>Babu boye-boye sunga gurbin Ronaldo a wasan

Bayan da Real Madrid ta buga babban wasanta na farko tun bayan tafiyar Cristiano Ronaldo wanda ya kare tana shan kashi a hannun Atletico Madrid daci 4-2, Tauraron dan wasanta, Casemiro  yace, wannan wasa ya tabbatar da cewa Ronaldo ne na daya a Duniyar kwallo kuma sun yi kewarshi.


Bayan kammala wasan, Casemiro ya bayyanawa manema labarai cewa, babu boye-boye Wannan wasan da mukayi ya tabbatar da cewa Ronaldo shine gwani na daya a harkar kwallo a Duniya kuma tabbas munga gurbinshi.

Amma ba zamu ta yin maganar rashin Ronaldo ba, dole mu rungumi kaddara  mu ci gaba daga inda aka tsaya mu kuma mayar da hankali kan 'yan wasan da muke dasu yanzu.

Akan sabon me horas da 'yan wasan na Real Madrid da kuma sakamakon da suka samu, Casemiro yace, yayi wuri a fara maganar ko Julen yayi kokari ko kuwa a'a domin kuwa yanzu muka fara wasa. Kuma bani da wanda zance laifinshine wannan rashin nasarar da mukayi saboda idan mukayi nasara,mu duka ne mukayi nasara haka idan mukayi rashin nasara shima mu duka ne mukayi rashin nasara.

Julen Lopetegui dai shine me horas da 'yan wasa na farko na kungiyar Real Madird da yayi rashin nasara a wasanshi na farko tun shekaru 11 da suka gabata.

Masu sharhi ma dai sunce, ko da me horas da 'yan wasan na Madrid na da laifi a wannan rashin nasara da sukayi to bashi da yawa domin kuwa bawai rashin Ronaldo kawai ne ya bayyana a wasan na jiya ba, hadda sakacin 'yan wasan baya da suka yi ta bandam-bandam da ya kai ga Costa yayi ta wasan kura dasu yana samun damarmaki.

Shima me horas da 'yan wasan na Madrid, Julen Lopetegui ya bayyana cewa, yayi matukar bakin cikin rashin nasarar da yayi amma zasu koma su shiryawa gasar Laliga da za'a fara a karshen makonnan.

Yace sunyi kokari amma da Atleico Madrid sukaci kwallo ta 3 sai 'yan wasanshi suka shiga rudani, suka fara neman kwallo ido rufe, daga nanne sai wasansu ya kara dabarbarcewa wanda kuma koda wanenen haka ne zata faru dashi.

Marca ta ruwaito cewa an tambayi Julen akan rashin katabus da Gareth Bale yayi lokacin da wasa yayi nisa, sai ya kada baki yace, ba sabon abu bane ganin 'yan wasa basu da cikakken kuzari a irin wannan lokaci na farkon kakar wasa amma munyi farin ciki da irin wasan da yayi kuma muna fatan zai akara kaimi nan gaba.

No comments:

Post a Comment