Saturday, 11 August 2018

Bazai yiwu a tsihe Buhari ba muna a majalisa>>Shehu Sani

A makon daya gabatane jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu yayi zargin cewa, ana wata makarkashiya ta tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari a majalisar tarayya, saidai sanata Shehu Sani ya bayyana cewa muddin akwai irinsu a majalisar to hakan ba zata taba yiyu ba.


Ga abinda ya fada, kamar yanda Rariya ta ruwaito:

"Harsashen da shugaba Tinubu ya yi na makarkashiya da ake yi na tsige Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai ma taba yiwu wa bane, muddin irin mu na cikin wannan Majalisa. Idan ma da wani ko wata da ke tunanin haka, a shirye muke, muna jira mu kara Ga fili ga mai Doki".

No comments:

Post a Comment