Monday, 27 August 2018

Bazan sake ganawa da Buhari ba har abada saboda bashi da kuzari>>Shugaban Amurka Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya shaida wa hadimansa cewa ba ya fatan sake ganawa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari saboda "ba shi da kuzari."


A watan Afrilu ne shugabannin biyu suka gana a fadar White House - ziyarar da a wancan lokacin kakakin Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana a matsayin amincewar da gwamnatin ta yi wa gwamnatin Najeriya.

Sai dai jaridar Financial Times ta Burtaniya ta ambato wasu majiyoyi uku da ba sa son a fadi sunansu suna cewa Shugaba Trump ya shaida musu cewa "har abada ba ya son sake ganawa da Shugaba Buhari saboda ba shi da kuzari."

Ranar Litinin ne ake sa ran shugaban na Amurka zai gana da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta inda za su tattauna kan harkokin kasuwanci da tsaro.

"Trump mutum ne bai son walwala. Nahiyar Afirka ba ta jan hankalinsa amma idan aka samu mutum kamar [Kenyatta] zai sa ya mayar da hankali kan nahiyar," a cewar wasu jami'ai da ke kulla alaka tsakanin Amurka da Kenya wadanda ba sa so a ambaci sunayensu.

Mr Buhari shi ne shugaban kudu da yankin hamadar Afirka na farko da Mr Trump ya gayyata fadar White House, matakin da ake gani ya dauka ne saboda Najeriya ce kasar da ta fi fitar da danyen man fetur a Afirka ga kasashen duniya.

Shugaba Trump dai ya saba yin katobara, domin kuwa a bara ma ya bayyana nahiyar Afirka a matsayin wata "salga."

Ganawar da Shugaba Buhari ya yi da Shugaba Trump ita ce karo na biyu da shugabannin Amurka suke gayyatar sa Fadar White House.

A shekarar 2015, tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya taba gayyatar shugaban na Najeriya zuwa Washington.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment