Tuesday, 21 August 2018

Bikin Sallah: An rufe wuraren shakatawa a Kaduna

Gwamnatin Kaduna ta bayar da umurnin rufe dukkanin wuraren shakatawa da wasan yara a tsawon lokacin bukukuwan Sallah a jihar.


Hukumomin jahar cikin wata sanarwa sun bayyana fargabar tsaro a matsayin dalilin daukar matakin.

Kanal Yusuf Yakubu mai bai wa gwamnan Kaduna shawara kan sha'anin tsaro ya shaidawa BBC cewa tsoron fitina ne ya sa suka dauki matakin rufe wuraren shakatawar.

Sai dai kuma ya ce za a yi hawan Sallah da aka saba yi kowacce shekara a masarautu na jahar, yana mai cewa gwamnan jihar zai yi hawan Sallah a Kafanchan.

Wakilin BBC ya ce bisa al'ada wuraren shakatawar sukan cika makil da matasa, yara maza da mata da iyalai a lokacin bukukuwan Sallah da na Kirsimeti.

Wasu dai mutanen jihar sun yaba da matakin wanda suka ce zai hana kashe-kashen da ake samu tsakanin matasa a wajen shakatawar a lokacin bukukuwan Sallah yayin da kuma wasu ke cewa matakin takura ce ga jin dadi da kuma walwalarsu.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment