Wednesday, 8 August 2018

BUHARI BAI TSINANA MANA KOMAI BA>>SARKIN DAURA

Mai martaba sarkin Daura, Dr. Umar Faruq Umar, a ranan Litinin ya ce jama'arsa da mutanen Daura na cikin halin kunci duk da cewa dansu, shugaba Muhammadu Buhari, ne shugaban kasa.


Ya bayyana hakan ne yayinda yake jawo hankalin ministocin da suka amfana da matsayin da shugaba Muhammadu Buhari ya basu na su kawo agaji masarautar ta ayyuka da noma.

Sarkin ya yi jawabi ne lokacin da ya karbi bakuncin ministan noma da raya karaka, Dakta Audu Ogbeh, wanda ya kai ziyarar ban girma fadar sarkin a garin Daura.

No comments:

Post a Comment