Tuesday, 7 August 2018

Buhari ne ya bayar da umarnin tsige Daura bayan gano wata makarkashiya tsakaninsa da Saraki

Sahara Reporters ta wallafa wani labara dake bayyana cewar saida mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya samu sahalewar Buhari kafin ya salami shugaban hukumar DSS, Lawan Daura, daga aiki.


Jaridar ta wallafa cewar tun da misalign karfe 4:00 na safiyar ranar Talata osinbajo ya samu amincewar Buhari a kan sallamar Daura daga aiki.

A cewar Sahara, shugaba Buhari ya gano cewar Daura da Bukola na aiki tare domin bata sunan gwamnatinsa a gida Najeriya da ma duniya baki daya.

Majiyar Sahara ta shaida mata cewar hatta mamaye harabar ginin majalisa da jami’an hukumar DSS suka yi, wani yunkuri ne da Daura ya yi domin nemawa Saraki suna ta hanyar nuna gwamnati na muzguna masa saboda ya fita daga jam’iyyar APC.

Tuni fadar shugaban kasa ta bayyana cewar babu hannun shugaba Buhari ko na mataimakinsa a yunkurin jami’an tsaron hukumar DSS hana shiga ginin majalisar a yau, Talata.

No comments:

Post a Comment