Thursday, 2 August 2018

Buhari ya bada umarnin gina titi mai hannu 10 a Legas

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da gina wani katafaren titi mai hannuwa goma a jihar Legas akan kudi naira biliyan saba’in da biyu da miliyan dari tara, (N72.9bn), kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.


Ministan ayyuka, Babatunde Fashola ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 1 ga watan Agusta, inda yace Buhari ya amince da aikin ne a yayin taron majalisar zartarwa da ake yi kowanni sati.

Fashola yace wannan aiki za’ayi shi ne a sake gina babbar hanyar da ta taso daga Apapa zuwa farkon shiga jihar Legas, wani sashi na babbar hanyar Legas zuwa Ibadan, inda yace hakan zai magance cunkoson ababen hawa da ake yawan samu akan titin.

“Ma’aikatar ayyuka, lantarki da gidaje ta samu izinin sake gina titin da ya hada Creek-Tin Can island-oworoshoki har zuwa farkon shiga Legas, an yi wannan hanya ne don manyan motoci su fita ba tare da sun bi ta cikin gari ba, a yanzu kam ya lalace, don haka aka amince a sake gina shi akan kudi N72.9bn.” Inji Fashola.

Fashola yace za’ayi aikin ne akan tsarin hadin gwiwa da yan kasuwa, inda yace gwamnati ta bada kwangilar gina hanyar ga kamfanin Dangote, ya kara da cewa titin zai hada da hannuwa goma, guda biyar a kowanne bangare, tsawonsa ya kai kilomita 270.8, kuma zai kunshi magudanan ruwa, gadoji, gyaran gadoji dake hanyar da kananan hanyoyi.
Dailynigerian.

No comments:

Post a Comment