Tuesday, 21 August 2018

Buhari ya ce hakura da yaki da rashawa cin amanar 'yan Najeriya ne

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai hakura da yaki da cin hanci da rashawa ba duk da ya janyo ma sa kiyayya da bakin jini ga wasu.


A cikin sakonsa na sallah ga al'ummar Najeriya mai dauke da sa hannun mai taimaka wa shugaban na musamman kan yada labarai Malam Garba Shehu, shugaban na Najeriya ya bukaci dukkanin musulmi su yi amfani da wannan damar domin yi nazari da yin karatun ta-natsu tare da kasancewa jekadu nagari ga addininsu ta hanyar yin aiki da koyarwarsa.

Buhari ya kuma bayyana cewa adddini wani abu muhimmi ne da ke tasiri ga halayen mutum da kuma ayyukansa.

A cikin sakon na Sallah, shugaban ya kuma bayyana damuwa da nadama kan yadda ya ce, son kai da hadama da cin hanci da rashawa ya sa wasu sun yi watsi da imaninsu domin cimma burinsu na rayuwa.

"Mika wuya ga yaki da rashawa ba zabi ba ne domin yana lalata al'umma da ci gaban kasa."
A cewar shugaban, " ko da kuwa yaki da rashawa ya janyo maka bakin jinni ga wasu, ba zai sa ka kariya ba a matsayinka na shugaba domin yin hakan tamkar cin amana ne ga jama'a."

Shugaban ya bukaci 'yan Najeriya su rungumi hanyoyi na tabbatar da zaman lafiya da hakuri da juna a kowane lokaci ta hanyar kawar da son zuciya da duk wasu bukatu na akidu ko kuma kungiyoyi.

A sakonsa na sallah ga Al'ummar musulmi, kakakin majalisar wakilai Hon Yakubu Dogara ya yi kira ga shugabannin addinai da su yi amfani da wannan lokaci domin fadakarwa kan zaman lafiya da hadin kai tsakanin 'yan Najeriya musamman yanzu da aka shiga lokaci na siyasa yayin da zaben 2019 ke karatowa.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment