Sunday, 19 August 2018

Buhari ya ce zai daure barayi da dama

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa kasar daga hutu shi ne daure barayi.


Shugaban ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talbijin na NTA jim kadan bayan ya isa fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban birnin kasar.

Da aka tambaye shi game da abin da zai sa a gaba bayan ya yi hutun kwana goma, Shugaba Buhari ya ce "za mu daure barayi da dama wadanda suka jefa mu cikin matsin tattalin arziki. Da ma na san ana sa ran zan yi hakan, kuma zan yi."

Yaki da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da Shugaba Buhari ya yi alkawarin aiwatarwa lokacin da yake yakin neman zabe.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment