Tuesday, 28 August 2018

Buhari ya janyowa Najeriya zubewar kima a duniya>>PDP

Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta zargin shugaban kasar Muhammadu Buhari da zubar da kimar kasar yayin ziyarar da ya kai Amurka wadda ta kai shi ga ganawa da Donald Trump.


Kalaman na PDP cikin sanarwar da ta fitar da ke matsayin martinin kan kalaman Donald Trump da ya bayyana Buharin da maras kuzari na zuwa ‘yan sa’o’i kalilan bayan wata jarida a Amurka ta wallafa labari wanda ke cewa Trump ya fatan ka da ya kara ganawa da mutum makamancin shugaban Najeriya.

Acewar PDP kalaman na Trump makoma ce ga kasashen da suke da shugabanni marasa kima wadanda saboda gazawa ke zagayawa don neman goyon bayan shugabannin kasashen duniya.

Sanarwar ta PDP ta bakin skataren yada labaranta na kasa Kola Ologbondiyan ta kalaman na Donald Trump ba wai cin zarafi ne ga Buharin shi kadai ba face ga kasar baki daya, duk kuwa sakamakon wuce kimar ta shuagba Buhari.

Babbar Jam’iyyar adawar ta PDP ta ce tana bukatar ta ji martini daga ilahirin bangarorin Fadar shugaban na Najeriya da kuma fadar shugaban Amurka kan batun wanda wata Jarida a Amurka ta wallafa tana mai cewa Buharin ya kai kasar ga fuskantar cin zarafi mafi muni daga ketare.
RFIHausa.

No comments:

Post a Comment