Wednesday, 8 August 2018

Burnley ta sayi golan Manchester City a kan fam miliyan 3.5

Burnley ta sayi golan Manchester City Joe Hart a kwantaragin shekara biyu a kan fam miliyan 3.5.


Shugaban kungiyar Sean Dyche ya sayi golan ne tare da saurarn gololi biyu wato Nick Pope da Tom Heaton.

Hart, wanda ya yi wa kasar Ingila wasanni 75, ya kuma yi wa City wasanni 350, inda suka lashe kofin Firimiya biyu da kuma Kofin FA daya.

Golan ya fara nuna sha'awar barin City ne tun bayan da Kocin Kungiyar Pep Guardiola ya rika ajiye shi a benci.

Sau daya Hart ya kama wa City gola tun bayan da Guardiola ya zama kocin kungiyar a shekarar 2016.

Ya kuma kwashe kaka biyu a matsayin aro a kungiyar Torino da kuma West Ham.

Hakazalika kasar Ingila ba ta je da shi gasar cin kofin duniya da aka yi a kasar Rasha a shekarar 2018.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment