Tuesday, 28 August 2018

Chelsea ta musanta labarin cewa Roman Abramovic zai sayar da ita

Bayan da rade-radi suka yi karfi akan cewa me kungiyar Chelsea, Roman Abramovic na shirin sayar da kungiyar akan kudi mafi tsada da aka taba sayar da wata kungiyar kwallo tun bayan Manchester United, Chelsean ta fito ta musanta wadannan rahotanni.


Me kungiyar dai yana tsaka da rashin jituwa da gwamnatin kasar Ingila bayan da suka hanashi bizar shiga kasar, shi kuma ya nufi kasar Isra'ila ya yanki katin zama dan kasa, dalilin hakane wata majiya ta bayyana cewa Abramovic wanda attajirin gaske ne dan kasar Rasha ya saka Chelsea a kasuwa yana neman Yuro miliyan dubu 2.5.

Saidai wani rahoto da ya fito daga jaridar The Mirror ya bayyana cewa Chelsea tace me kungiyar yana nan kan ra'ayinshi na rike Chelsean bazai sayar da itaba.

No comments:

Post a Comment