Sunday, 12 August 2018

Cikin mintina 8 da fara wasa, Ronldo ya ciwa Juventus kwallo ta farko

A karin farko tun bayan komawarshi Juventus, Cristiano Ronaldo ya buga mata wasa na farko kuma ya ci kwallon shi ta farko cikin mintuna 8 kacal da fara wasa.


Wasan da aka buga yau Lahadi an yishine tsakanin manyan 'yan kwallon Juventus din da matasan 'yan kwallo na kungiyar, dama al'adace ta kungiyar buga irin wannan wasa ga duk wani sabon dan wasa da ta siya, inda take nunawa masoyanta shi.

Ronaldo daizai buga wa Juven wasan farko da zata buga da wata kungiya ta daban ranar 18 ga wannan watan da muke ciki.

Wannan kwallo da yaci tasa ya samu yabo sosai.

No comments:

Post a Comment