Thursday, 16 August 2018

Cikin shekaru 18, Madrid tayi rashin nasara a wasan karshe a hannun Atletico Marida da ci 4-2: Ramos ya maye gurbin Ronaldo

Real Madrid tasha ruwan kwallaye har hudu a hannin Atletico Madrid a wasan da suka buga jiya, Laraba wanda ya baiwa Atletico Madrid din nasarar cin kofin Super Cup, wasan dai ya kare da sakamakon 4-2.


An kare lokacin wasan 2-2 wanda hakan yasa dole aka kara lokaci inda ananne Atletico Madrid, bayan kwallayen da Diego Costa yaci guda biyu 'yan wasanta Saul Niguez da Koke Saw suka ci mata karin kwallaye biyu.

Kwallon farko da Costa yaci cikin sakwanni 49 da fara wasa itace kwallo da aka taba ci cikin mafi kankanin lokaci a tarihin gasar ta Super Cup, sannan a shekaru 18 da suka gabata, wannan ne karo na farko da Real Madrid tayi rashin nasara a wasan karshe na duk wata babbar gasar kasa da kasa data taba kaiwa.

Ta bangaren Real Madrid kuwa, Karim Benzema ne yaci musu kwallo ta farko sannan sai Sergio Ramos yaci musu ta biyu a kwallon daga kai sai me tsaron gida da ya buga, kwallon da Ramos yaci tasa masu sharhi suka bayyana cewa, ta wajan buga kwallon daga kai sai me tsaron gida, Ramos din ya maye wa Madrid rashin Ronaldo.

No comments:

Post a Comment