Saturday, 4 August 2018

Cristiano Ronaldo ya daina bibiyar Real Madrid a shafukan sada zumunta

Tauraron dan kwallon kafar kasar Portugal daya koma bugawa Juventus wasa daga tsohuwar kungiyarshi ta Real Madrid, ya daina bibiyar Real Madrid din a shafin sada zumunta na Instagram inda ya koma yana bibiyar sabuwar kungiyarshi ta Juventus.


Jaridar Metro UK ta ruwaito cewa, dan kwallon ya yanke duk wata alaka da tsohuwar kungiyar tashi ta Real Madrid

No comments:

Post a Comment