Saturday, 4 August 2018

'Da nine Ganduje sai na farraka tsakanin Kwankwaso da Shekarau'

Siyasa rigar 'yanci amma fa bahaushe yace kyan dara kasawa,dan haka a duk sanda zabe yazo 'yan siyasa musamman a Nigeria, sukan mayar da hankali ne wajen bin duk wata hanya da zata kai su ga Samun nasara. (idan akwai kuskure a gyara min) nasan wasu'yan siyasar ma har kisa sukan iya yi matukar dai bukata zata biya.


To a saboda da haka ne nake ganin cewar tun da lissafi ya zo a cakwalkwale,Kano ta tasamma zama babu tabbas to idan Laila ta kiya sai a koma Basha, domin durkusawa wada ba gajiya wa ba ne. 

Dan haka DA NINE GANDUJE da na zauna da Mal Shekarau mun kulla kawance, kuma da nine Ganduje ba anan zan tsaya ba sai nayi tattaki zuwa Abuja na gana da Shugaba Buhari na roke shi yayi hakuri su sasanta sabanin su da Mal Shekarau, domin hakan wata hanya ce ta tsira, haka kuma da nine Ganduje duk abin da za'ayi sai naga na dinke wannan baraka domin ita ce dama ta mai dama-dama, wajen magance fargabar taron dangi da ake shirin yi min a 2019.

DA NINE GANDUJE da ba zan taba yarda da masu yi min dadin bakin cewar hadin gambizar Kwankwaso da Shekarau ba barazana ne gare ni ba.

DA NINE GANDUJE da bazan taba samun nutsuwa ba matukar zan cigaba da neman tazarce har sai naga na farraka tsakanin Kwankwaso da Shekarau domin nasan haduwar su inuwa guda matsala ce gare ni.

Bahaushe dai yace da asara gara gidadanci, na san dai sai mai kaifin basira ne kadai yake iya gane furfurar farar tunkiya.
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment