Thursday, 9 August 2018

Da sanin Buhari aka kori Lawal Daura>>Fadar shugaban Najeriya

Mai taimaka wa shugaban Najeriya kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya ce kan Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osinbajo a hade yake.


Femi Adesina ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake gana wa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta kasar wanda aka yi a fadar shugaban kasar da ke Abuja ranar Laraba.

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ne ya shugabanci taron.

Shugaba Buhari ya fara hutun kwana 10 ne a birnin Landan ranar Juma'a.

Bayan an kammala taron, manema labarai sun tambayi Mista Adesina ya fayyace musu ko Shugaba Buhari na da masaniya a kan korar da mukaddashin shugaban kasar ya yi wa shugaban hukumar tsaro ta farin kaya DSS Lawal Daura.

Mista Osinbajo ya sallami Lawal Daura ne bayan da wadansu jami'an hukumar DSS wadanda suke rufe fuskokinsu sun hana wadansu 'yan majalisar kasar shiga zauren majalisar a ranar Talata.

Mista Adesina ya ce kawunan shugabannin hade yake kuma babu wata baraka tsakaninsu.

Ya bayyana cewa dukkan lokacin da shugaban kasa zai tafi hutu, ya kan mika ragamar mulki ga mataimakinsa.

Kuma daga lokacin mataimakin ya zama mukaddashin shugaban kasa mai cikakken ikon da shugaban kasa ke da shi.

Har ila yau, ya ce a wannan karon ma Sshugaba Buhari ya dauki wannan matakin na mika masa ragamar kasar.

A karshe ya ce akwai kyakkyawar fahimta tsakanin shugabannin biyu, kuma daukan wannan mataki da aka yi ba abu ne da za a iya tattauna shi a gaban manema labarai ba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment