Saturday, 25 August 2018

Dalilin da ya sa na tsunduma a harkar fim din Hausa>>Jamila Nagudu

Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana'antar shirya fina-finan Hausa da ake yi wa lakani da Kannywood watau Jaruma Jamila Umar da aka fi sani da Jamila Nagudu ta bayyana dalilin da ya sa ta tsunduma a cikin harkar fim.


Jarumar dai ta bayyana hakan ne a lokacin da take fira da majiyar mu ta Muryar Amurka a watannin baya a cikin shirin su na duniyar Kannywood inda ta ce ta fara sha'awar yin fim ne bayan da ta kalli wani fim a shekarun baya inda a ciki aka nuna halin wata mata maras kyau da ke kama da na wata makwaficiyar ta da kuma irin yadda karshen ta ya kasance.

Jarumar wadda yanzu haka tana cikin 'yan fim masu tsada da kuma aji ta bayyana cewa daga wannan lokacin ne ta fahimci cewar lallai masu yin fim fadakarwa suke yi shine ma ita ta shigo domin ta bada gudummuwar ta.

Yan fim din Hausa dai a lokuta da dama suna fuskantar kyama da tsangwama daga al'ummar da suke cikin su sakamakon kallon da ake yi masu na masu bata tarbiyyar mutane, zargin da a kullum suke karyatawa.
Naija.ng.

No comments:

Post a Comment