Friday, 17 August 2018

Dalilin da yasa Gwamnatin Buhari bata rabawa mutane tsabar kudi>>Lai Muhammad

Da yake magana lokaci daya je rangadin sake ginawa da gyaran titin Ilorin zuwa Jebba zuwa Mokwa, Ministan watsa labarai da al'adu, Lai Mubammad yace, suna sane da kukan da wasu 'yan Najeriya keyi na rashin kudi da tsadar rayuwa amma akwai dalilin da yasa basu ba mutane tsabar kudi kyauta.


Ya kara da cewa, gwamnatinsu ba irin wadda ta shude bace, ba zasu rika rabawa mutane tsabar kudi a hannu ba, sun kwammace su yi aikin raya kasa wanda zai inganta rayuwar al-umma kowa ya amfana.

Ya bayar da misalin cewa yanzu kunga titinnan, a shekarun baya lokacin da gwamnati ke rabawa mutane kudi, manyan motoci na kwashe kwanaki biyar kamin su kai Ilorin daga Jebba amma gyaran da muka mishi yanzu cikin awanni kalilan zaka je inda kake so.

Yace da ace kudin da akayi gyaran titinnan rabawa mutane mukayi, wasu ne kalilan zasu samu kudin kuma idan aka tashi zagin mu akan cewa bama aiki haddasu za'a hadu a zagemu.

Amma yanzu gashi anyi abinda kowa zai amfana kuma tattalin arziki ya habaka.

Yace shi yasa mun zabi gyaran abubuwan inganta rayuwar Al'umma a hankali fiye da raba kudi.

No comments:

Post a Comment