Thursday, 16 August 2018

Dalilin da zaisa inyi takarar shugaban kasa da Buhari>>Saraki

Kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki ya bayyana cewa, zata iya yiyuwa fa ya shiga sahun masu neman kujerar shugaba kasa a zabe me zuwa na shekarar 2019 idan Allah ya kaimu.


Saraki dai ya bayyana hakane a hira da yayi da jaridar Bloomberg inda ya bayyana cewa yana nan yana tuntubar jama'a da masana akan wannan magana.

Ya bayyana cewa babban dalilin da yake so ya tsaya takara shine, ya tabbatar da cewa zai iya kawo canjin da ake ta muradin samu a Najeriya.

Saidai a kwanakin baya, Saraki ya karyata ikirarin shahararren dan jaridarnan, Dele Momodu da yayi cewa zai fito takarar shugaban kasa a zaben 2019, inda yace da hakane da tuni anga labarin ya karade manyan jaridun kasarnan.

Saraki dai ya canja sheka daga jam'iyya me mulki ta APC zuwa PDP kuma ya tabbatarwa da jaridar Bloomberg cewa idan zai tsaya takara a jam'iyyar PDP dinne zai yita.

No comments:

Post a Comment