Wednesday, 29 August 2018

Dan Cristiano Ronaldo ya shiga kungiyar kananan yara ta Juventus

Masu iya magana na cewa kyan da ya gaji Ubansa, irin hakane ta faru da dan tauraron dan kwallonnan dake bugawa kungiyar Juventus wasa, watau Cristiano Robaldo, dan na Ronaldo yanzu haka dai ya shiga kungiyar kananan yara ta Juventus din inda ya fara atisaye dasu.


Football Italia ta ruwaito cewa, anga dan na Ronaldo yana atisye da kungiyar yara 'yan kasa da shekaru tara na Juventus din. Wannan na zuwane kwanaki kadan bayan da Ronaldo ya bayyanawa DAZN cewa yana da tabbacin cewa dan nashi zai gajeshi.

No comments:

Post a Comment