Saturday, 18 August 2018

Dan Fim Din Hausa, Tijjani Faraga Ya Tsinci Katafariyar Wayar Wani Matashi Ya Mayar Masa Da Ita

Dan Wasan Hausan Malam Tijjani Faraga, Ya Tsinci Wayar Ne Kirar IPhone A Wurin Wani Babban Taro Da Aka Gabatar A Babban Dakin Taro Na Shoprite Kano, Kuma Nan Take Ya Nemi Mai Wayar Domin Ba shi Abarsa. 


Matashin Da Ya Wullar Da Wayar, Ya yi Mutukar Farin Ciki Domin A Cewar Mai Wayar Wannan Ne, Karo Na Hudu Yana Wullar Da Wayarshi Amma Kuma  Wannan Ne Karo Na Farko Da Aka Taba Dawo Masa Da Ita. 

Matashin Da ya Wullar Da Wayar Ya yi Alkawarin Gayyatar Malam Tijjani Faraga Domin Karrama shi.
Rariya.

No comments:

Post a Comment