Friday, 24 August 2018

Dan gani kashenin Kwankwaso ya koma bayan Buhari

A jiya kenan Yayin wata ziyara ta barka da sallah da ya kaiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa dake Garin Daura A jihar katsina.Hon. Abubakar Abdullahi lado dai dan majalisar wakilai ne daga jihar Neja mai wakiltar garuruwan Gurara, Suleja,da kuma Tafa duk a jihar Neja.

Kuma hasali Lado dai Rikakken dan Kwankwasiyyane kamar yadda kowa ya sani a  baya, yanzu kam ga dukkan Alama yayi jifa da jar hula yabi tafiyar baba Buhari, kamar yadda kuka gani akan sa ba jar hula, kuma ga baba ya daga hannun sama.

Daga Real Sani Twoeffect Yawuri

No comments:

Post a Comment