Wednesday, 22 August 2018

Dan kasar Chinan nan daya musulunta ya halarci sallar Idi a karin farko

A kwanannanne mukaji labarin wani dan kasar Chaina daya musulunta har ya samu matar aure a garin Wase dake jihar Filato, wannan hoton shine a lokacin da yake halartar Sallar Idin babbar Sallah jiya.


Dan kasar Chinan ya saka kaya, babbar riga da hula.

Jaridar rariya ta ruwaito cewa, dan kasar Chinan yace, Ina Kira Sauran 'Yan Uwana 'Yan Chana Da Suka Shigo Addinin Musulunci.

Muna fatan Allah ya karomana irinshi, shi kuma ya kara fahimtar dashi addini.

No comments:

Post a Comment