Saturday, 4 August 2018

Dan kirki ne aka mayar da shi mai tsattsauran ra'ayi a makaranta>>Mahaifiyar Osama

Mahaifiyar marigayi Osama Bin Laden, wanda ya shugabanci kungiyar al Qaeda ta yi magana a karon farko shekaru bakwai bayan mutuwarsa a 2011.


Alia Ghanem ta yi hira da jaridar Guardian ta Birtaniya daga gidansu da ke birnin Jidda a kasar Saudiyya.

Ta fada ma jaridar cewa dan nata mai kunya ne kuma mai kyawawan halaye a lokacin da yake tasowa, amma daga baya ta ce an juya masa tunani a jami'a.

Iyalansa sun ce a shekarar 1999 ne suka yi tozali da shi a karo na karshe, shekara biyu kafin harin 11 ga watan Satumba a lokacin yana Afghanistan.

"Batun ya tayar mana da hankali matuka. Ban so irin wannan abin ya faru ba. Saboda me yayi watsi da rayuwarsa baki daya? inji uwargida Ghanem da aka tambayeta yaya ta ji da aka ce dan nata ya zama dan gwagwarmayar addinin Islama?

Iyalan Bin Laden na da karfin fada a ji a kasar saudiyya, bayan da suka tara makudan kudade daga harkar gine-gine.

Mahaifin Bin Laden Mohammed bin Awad bin Laden ya saki Alia Ghanem shekara uku bayan an haifi Osama, kuma 'ya'yansa sun kai 50.

Bayan harin 9 ga watan Satumba, iyalan Bin Laden sun ce hukumomin Saudiyya sun yi ta masu tambayoyi, kuma daga baya an takaita masu tafiye-tafiye.

Dan jaridan da ya gudanar da ganawar, Martin Chulov ya ce Saudiyyar ta kyale shi yayi wannan hirar da uwargida Alia Ghanem ne saboda duniya ta shaida cewa Osama fandararre ne a cikin dangi.

Ya ce wannan kuma dama ce ta nuna cewa Osama ba yana ma daular Saudiyya aiki ba ne, kamar yadda wasu ke ikirari.

'Yan uwan Osama su biyu Hasaan da Ahmad sun halarci wannan hirar da jaridar Guardina din ta yi, kuma suma sun bayyana tashin hankalin da suka shiga da aka sanar da su cewa Osama na da hannu wajen kai hare-haren na 11 ga watan Satumba.

"Dukkanmu babba da yaro mun ji kunyar wannan abin da yayi. Mun kuma san cewa zamu dandana kudarmu. Iyalan gidanmu da ke kasashen waje duk sun dawo gida", Ahmad ya fada ma jaridar.
BBCHausa.

No comments:

Post a Comment