Friday, 17 August 2018

Daruruwan Pasto sun yi wa dubunnan yara kanana fyade a Amurka

A jihar Pennsylvania ta Amurka an gano cewar daruruwan malaman Chochin Katolika sun yi fyade ga dubunnan yara kanana.


Sakamakon rahoton cin zarafin yaran da aka aka fitar Fadar Vatican ta bayar da sanarwa tare da sukar Pastocin da suka yi wannan ta'asa inda ta ce, wannan mummunar dabi'a ce da ya kamata a yi Allah Wadai da ita.

Daraktan Ofishin Yada labarai na Vatican Greg Burke ya sanar da cewa, suna la'antar wannan cin zarafin yara na yi musu fyade da pstoci suka yi.

Burke ya rawaito da aka fitar a Pennsylvania da ke cewa "Kalmomi biyu ne kawai za a bayyana wannan kazamin aiki da su kuma su ne: Abun kunya da bakin ciki."
TRThausa.

No comments:

Post a Comment