Monday, 6 August 2018

Daso ma ta samu kyautar kujerar Makka daga matar gwamnan jihar Kebbi

A jiyane mukaji yanda tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta fito take godewa matar gwamnan jihar Kebbi, Dr. Zainab Atiku Bagudu bisa kyautar kujerar Makka da ta mata. Saratu Gidado ma wadda akafi sani da Daso ta yiwa Dr. Zainab godiya da kyautar kujerar makar data mata.Daso ta saka wadannan hotunan da take a jirgin sama da kuma a lokacin da take a Madina, ta bayyana cewa tana godewa Allah da wannan dama da ta samu da kuma matar gwamnan jihar Kebbi da wannan kyauta da ta mata.

Muna fatan Allah yasa ayi Ibada karbabbiya ya kuma dawo dasu gida lafiya.

No comments:

Post a Comment