Saturday, 4 August 2018

Denmark ta ci tarar wata mata kan saka nikabi

A karon farko Denmark ta ci tarar wata mata bayan ta karya dokar haramta rufe fuska a bainar jama'a.


Matar mai shekara 28 da ke sanye da nikabi ta hadu ne da wata mata a wani kanti a arewacin Copenhagen wacce ta nemi ta yi amfani da karfi ta cire nikabin da ke fuskar matar, lamarin da ya janyo hankalin 'yan sanda bayan rikici ya barke a wurin.

'Yan sanda sun caji duka matan biyu da laifin kokarin yin barazana ga zaman lafiya tare da kuma dora tarar dala dari da hamsin kan matar da ke sanye da nikabin.

Sabuwar dokar ta haifar da zanga-zanga da suka, musamman daga kungiyoyin kare hakkin dan adam a Denmark.

Kuma ra'ayi ya banbanta tsakanin al'ummar kasar, yayin da wasu ke ganin dokar ta yi daidai wasu kuma sun kira ta da sunan "bakar doka."

A ranar Laraba ne dai dokar ta fara aiki a Denmark bayan ta samu amincewar majalisa a shekarar nan.

Sai dai dokar ba ta ambaci burka ba ko nikabi ba amma ta ce za a hukunta duk wanda aka kama ya yi amfani da mayafin da ya rufe fuska a bainar jama'a.

Wasu al'ummar musulmi a kasar sun ce ba za su mutunta dokar ba duk da akwai tara mai tsauri ga wanda aka sake kamawa ya saba dokar.

Kasashen turai da dama ne suka haramta sa nikabi ko burqa da rufe fuska a bainar jama'a wadanda suka hada da Faransa da Austria da Bulgeria da Jamus da Bavaria.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment