Thursday, 16 August 2018

Diyar gwamnan Kaduna, Balqis ta samu sakamakon kammala makaranta me kyau abin Alfahari

Diyar gwamnan jihar Kaduna, Balqiss Nasiru El-Rufai ta samu kyakkyawan sakamo daga makarantar Sakandire da ta kammala a babban birnin tarayya, Abuja, sakamakon jarabawar na Balqis ya nuna cewa ta samu maki mafi kyau a jarabawartata.Da yake bayyana farin cikinshi da wannan sakamakon jarabawar na diyarshi, gwamna El-Rufai yace, Alhamdulillahi, shekaru 19 da suka gabata ya auri mahaifiyar Balqis me suna, Asia Ahmad sakamakon jarabawartata yayi daidai da ranar aurensu, wannan ba karamin abin farin ciki bane, Allah yayi mata Albarka ya kuma kareta tare da iyalanmu da kasar mu baki daya. Ina tayaki murna diyata.
Muma muna tayata murna da fatan allah yawa rayuwarta Albarka da sauran matasan baki daya.

1 comment: