Saturday, 11 August 2018

'Dodo' Pogba ya taimaki Man Utd doke Leicester 2 -1

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya yaba wa "dodo" Paul Pogba bayan da dan wasan ya jagoranci kungiyarsa ga nasara akan Leicerster City a ranar farko ta gasar firimiyar Ingila na bana, inda ya jefa kwallon farko.


Dan wasan da a kwanan nan ake rade-radin zai koma Barcelona ya bayar da mamaki, kwanaki hudu bayan da ya soma atisaye tun daworsa daga gasar cin kofin duniya da kasarsa Faransa ta lashe.

Man Utd ta fara wasan da kafar dama a filinta na Old Trafford, inda ta sami bugun daga kai sai gola bayan da Daniel Amartey ya taba kwallon da Alexis Sanchez ya buga da hannunsa.

Nan take Pogba ya aika da ita cikin ragar Leicester bayan wani bugu da yayi mai ban sha'awa, kuma gola Kasper Schmeichel bai iya tare ta ba.

Daga baya dan wasan baya na United, Luke Shaw ya jefa tasa kwallon bayan da ya yi nasarar gyara kurosin din da Juan Mata ya aika cikin gidan Leicester.

Amma Leicester ma ta zura kwallo daya ta hannun Jamie Vardy wanda aka saka daga baya.
Pogba ya buga wasa na tsawon minti 84 kafin Marouane Fellaini ya maye gurbinsa.

Mourinho ya ce bai yi tsammanin Pogba zai iya dadewa a wasansa na farko ba:

"Pogba dodo ne. Mun yi tsammanin ba zai iya wuce minti 60 ba, amma sai ga shi ya wuce minti 80 ma."

Mourinho ya kara da cewa, "Zabin cigaba da buga wasan na Pogba ne. Na tambaye shi ko zai huta, amma sai ya ce gara ya cigaba da buga wasan".
BBChausa.

No comments:

Post a Comment