Thursday, 30 August 2018

Duba yanda aka raba rukuni na gasar zakarun turai 2018/19An fitar da jadawalin rukuni-rukuni da ke nuna yadda kungiyoyin gasar zakarun Turai da za su fafata a mataki na gaba a gasar .A rukunin A kungiyoyin da za su fafata sun hada da Atletico Madrid da Dortmund da Monaco da kuma Club Brugge.

Barcelona da Totettenham da PSV da kuma Inter Milan ne za su murza leda a rukunin B, yayin da rukunin C ya hada da PSG da Napoli da Liverpool da kuma Red Star Belgrade.

A rukunin D akwai Lokomotiv Moscow da Porto da Schalke da Galatasararay, yayin da rukunin E ya kunshi Bayern Munich da Benfica da Ajax da AEK Athens.


Man City da Shakhtar da Lyon da kuma Hoffenheim ne a rukunin F, yayin da Real Madrid da Roma da CSKA Moscow da kuma Viktoria Plzen ke rukunin G.

Shi kuma rukunin H yada da Juventus da Manchester United da Valencia da kuma Young Boys.

A ranar 18 ga watan Satumba ne za a fara fafatawa a gasar ta zakarun Turai.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment