Saturday, 18 August 2018

'Duk da Ronaldo be ci kwallo ba amma yayi kokari'

Bayan kammala wasan Serie A na yau tsakanin Juventus da Chievo wanda ya kare Juve na da nasara da ci 3-2 'yan kallo da dama sun tashi jikinsu sanyaye saboda gwaninsu, Cristiano Ronaldo beci kwallo ba, saidai me horas da 'yan wasa na Juve yace Ronaldon yayi kokari.


Massimiliano Allegri ya shaidawa Sky Sport cewa, duk da Ronaldo be ci kwallo ba amma yayi kokari sosai dan kuwa ya kai hare-hare ma su kyau sannan kuma kokarinshi ya damfara ne akan 'yan wasan dake tallafa mishi.

Massimiliano Allegri ya kara da cewa, kwanakin Ronaldo 7 kacal yana atisaye da su dan haka gaskiya yayi kokari amma suna fatan a wasa na gaba zai fi haka.

No comments:

Post a Comment