Tuesday, 7 August 2018

Facebook zai haska wasan Ronaldo na farko a Juventus kyauta

Wasan farko da Cristiano Ronaldo zai bugawa Juventus, na daga cikin jerin wasannin gasar La liga ta Spain, da kuma Seria A ta Italiya, wadanda za’a haska su kyauta, ba tare da biyan sisi ba, a dandalin sada zumunta na Facebook, a kasashen Birtaniya da kuma Ireland a kakar wasa ta bana.


Ronaldo mai rike da kambun gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, da ya lashe sau biyar, zai bugawa Juventus wasan farko ne a ranar 18 ga watan Agusta, a wasan Seria A da zasu fafata da kungiyar Chievo.

Cikin wata sanar wa da ‘Eleven Sports’ kamfanin da ke da alhakin bada izini ko lasisin haska wasanni na Birtaniya ya fitar, ya ce an cimma wannan yarjejeniya ce a yau Litinin 6 ga watan Agusta na 2018.

A karkashin yarjejeniyar da kamfanin na Eleven Sports ya cimma tsakaninsa da kamfanin Facebook, za a rika haska wasa guda a kowane mako, daga wasannin La Liga da Seria A a dandalin sada zumuntar na zamani.
Rfihausa

No comments:

Post a Comment