Friday, 31 August 2018

FIFA ta jinjinawa kungiyar Super Eagles ta Nigeria

Shugaban babbar hukumar kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA), Mr. Gianni Infantino, ya jinjinawa kungiyar kwallon kafa ta Nigeria, Super Eagles, mai horas da yan wasa Gernot Rohr, ma'aikatan kungiyar, jami'ai dama daukacin masoya, bisa kwazon da suka nuna a gasar kwallon kafa ta duniya na wannan shekarar da aka buga a Rasha.


A cikin wata sanarwa da ya aikawa shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Nigeria NFF, Amaju Pinnic a ranar alhamis, Infantino ya ce: "Zan yi amfani da wannan damar, wajen nuna tsantsar godiyarmu ga kungiyar kwallon kafa ta kasarku, a shiga gasar cin kofin kwallo ta duniya karo na 21, wanda hukumar FIFA ta shirya.

"Gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a wannan shekarar, gasa ce da tarihi ba zai manta da ita ba, kuma babban tarihin shine kasamcewar Super Eagles ta samu damar shiga gasar, wanda shine karo na 6 da kungiyar ta buga gasar.

"Hakika ina cike da farin ciki, zan kuma iya bugun kirji akan hakan, domin na halarci wasanni biyu da kuka buga tsakaninku da kasar Croatia da Iceland. Don Allah ka isar min da sakon bangajiyata ga duk wanda ya bada gudunmowarsa, musamman 'yan wasa da mai horas da su, Gernot Rohr, da jami'ai, ma'aikata da kuma uwa uba masoyan kungiyar.

"Irin wannan nasara bata samuwa sai idan anyi aiki tukuri, amfani da kwarewa da kuma bin dokokin da aka gindaya, hadi da nuna sha'awar buga wasan. Irin wannan namijin kokari da Super Eagles ta nuna, ya tabbatar da cewa akwai kyakkyawar makoma ga nasarar kungiyar a nan gaba"
Naija.ng.

2 comments:

  1. These articles and blogs are genuinely sufficiency for me for a day. judi poker

    ReplyDelete
  2. I have been intelligent for hours and I haven't gone through such awesome stuff. shop

    ReplyDelete